Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har ila yau Naseer Abu Sharif ya fadi cewa jajebarin cin nasarar Alummar falasdinu yana kara karatuwa sosai, yace Isra’ila tana ci gaba da gudanar da siyasar danniya da kashe alummar falasdinu amma wannan bai sanyaya guiwar yan gwagwarmayar ba wajen ci gaba da jajircewa ba duk da irin laifukan da take tafkawa
Da yake tsokaci game da yadda Amurka take nuna goyon bayan kasar Amurka ya yi bayani akan shahadar yar jaridar nan ta gidan talabijin din Aljazeera shirin Abu Akleh sakamakon harbinta da sojojin Isra’ila ta yi ya ce hukumomin na kasa da kasa ba su yi tir da wadanda suka aikata wannan mumumunan aikin ba.
342/